Dakarun sojin Turkiyya sun kassara 'yan ta'addar a ware na PKK/YPG a yankin Farmakan Reshen Zaitin da ke arewacin Siriya.
Shafin Twitter na Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ya sanar da cewa,
"AYankin Farmakan Reshen Zaitin wasu 'yan ta'ada 3 sun yi kokarin lalata zaman lafiyar da aka samu. Dakarunmu sun kassara su, kuma suna samun nasarar farmakan da suke kaiwa a yankin."