An kassara wasu 'yan ta'addar a ware na PKK/YPG 2 a lokacin da suka yi yunkurin shiga yankin Tafkin Zaman Lafiya da ke arewacin Siriya.
A sanarwar da aka fitar ta shafin Twitter na Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya an bayyana cewar, jaruman dakarun sojin Turkiyya sun kassara 'yan ta'addar a ware na PKK/YPG 2 a lokacin da suka yi yunkurin shiga yankin Tafkin Zaman Lafiya da ke arewacin Siriya don lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin da aka samu.
A yankin Reshen Zaitun ma an kassara 'yan ta'adda 17 bayan da suka kai hari tare da yin sanadiyyar Shahadar sojan Turkiyya 1.