An kassara 'yan ta'addar a ware na PKK 8 sakamakon farmakai ta sama da dakarun Turkiyya suka kai a arewacin Iraki.
Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta sanar da cewa, an kassara 'yan ta'addar a ware na PKK 8 bayan gano su da aka yi a yankin Avashin-Basyan da ke arewacin Iraki.
Sanarwar da aka fitar ta shain Twitter na Ma'aikatar ta kara da cewa,
"Za a ci gaba da kai farmakan har sai an ga bayan dan ta'adda na karshe."