An kassara wasu 'yan ta'addar a ware na PKK 6 a lokacin da suka yi yunkurin kai hari a yankunan Gara da Zap na arewacin Iraki.
Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta bayyana cewar ana ci gaba da kai farmakai kan 'yan ta'addar a ware na PKK.
Sanarwar ta ce "A yankunan Zap da Gara na arewacin Iraki, bayan bincike da sanya idanu an gano wasu 'yan ta'addar a ware na PKK 6 d suka yi shirin kai hari. An kuma kassara su nan take."