An kassara 'yan ta'addar PKK 3 a farmakan da sojojin sama na Turkiyya suka kai yankin Gara da ke arewacin Iraki.
A rubutaciyyar sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta Kasa (MSB) ta fitar a shafukan sada zumunta, an bayyana cewa ana ci gaba da yaki da ta'addanci da kuma yanke hukunci yadda ya kamata.
A cikin sanarwar an bayyana cewa "An kassara wasu karin 'yan ta'addar PKK 3 da aka gano a yankin Gara da ke arewacin Iraki sakamakon nasarar da farmakan sojojin saman Turkiyya suka kai.”