A wasu farmakai da aka kai ta sama a arewacin Iraki an kassara 'yan ta'addar a ware na PKK 2.
Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta fitar da sanarwa ta shafinta na Twitter cewa,
"Muna ci gaba da rugurguza kawunan 'yan ta'adda."
Sanarwar ta kara da cewa, dakarun Turkiyya ne suka kassara 'yan ta'addar bayan gano su a yankin Gara na arewacin Iraki.