An kassara 'yan ta'adda mata 2 a Afrin

An kassara 'yan ta'adda mata 2 a Afrin

Jami'an tsaron Turkiyya sun kassara 'yan ta'adda 2 da suka yi shirin kai harin bam a yankin Afrin na Siriya.

Ofishin Gwamnan Hatay ya sanar da cewa, dakarun Turkiyya ne suka kassara 'yan ta'addar mata mambobin PKK/YPG a lokacin da suka yi yunkurin kai harin bam na kunar bakin wake a yankin da ya ke da cunkoson jama'a.

Sanarwar da aka fitar ta ce, an samu nasarar kassara 'yan ta'addar ta hanyar hada kai da aiki tare da jami'an tsaron da ke yankin.

 


News Source:   ()