An kassara 'yan ta'addar kungiyar PKK 3 a arewacin Iraki.
A cikin sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Kasar (MSB) ta fitar ta shafinta na Twitter ta bayyana cewar, ana ci gaba da aiwatar da ayyukan magance 'yan kuniyar ta'addanci ta PKK.
A cikin sanarwar an ce,
"An gano 'yan ta'addar PKK 3, ta hanyar yin bincike da kuma sanya ido a yankin Hakurk da ke arewacin Iraki kuma aka kassara su ta farmakin da aka kai ta sama."
A Siriya, Rundunar Sojojin Turkiyya (TSK) sun yi nasarrar magance wasu 'yan ta'adda 2 na PKK / YPG waɗanda suka yi yunƙurin kutsa kai cikin wani Shirin Garkuwa.
A gefe guda, an kama 'yan ta'addar PKK 3 a yankunan Kars a ayyukan cikin gida.