A garin Jalalabad na kasar Afganistan, an harbe wasu mata 3 'yan jarida har lahira.
Matan na aiki da tashar talabijin ta Enikass TV.
Daraktan tashar Zalmai Latifi ya shaida cewa, an harbe matan a hare-hare 2 daban-daban da aka kai musu a kan hanyarsu ta komawa gida a kasa daga wajen aiki.
Asibitin Yankin Nangarhar ya tabbatar da mutuwar matan.
An fara gudanar da bincike kan lamarin.
Babu wani da ya dauki alhakin kashe matan.