A arewa maso-gabashin Afganistan an kai harin bam tare da kashe daya daga cikin manyan kwamandoji kuma mataimakin shugaban jam'iyyar Jumbush Pirim Kul Ziyayi.
Kakakin helkwatar 'yan sandan jihar Tahar, Halil Esir ya shaida cewa, an kai harin bam a kauyen Girdab na gundumar Rustak d ke jihar Tahar tare da kashe mataimakin shugaban jam'iyyar Jumbush Pirim Kul Ziyayi.
Esir ya shaida cewa, a lokacin da aka kashe Ziyayi yana kaiwa 'yan tawayen Taliban farmakai a kauyen, kuma har yanzu ba a san ta yaya aka kai masa harin bam din ba.
Esir ya kara da cewa, an jikkata masu tsaron lafiyar Ziyayi 2 a harin.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.