A garin Aden na Yaman an aikata kisan gilla ga kwamishinan 'yan sandan jihar Hudeyde Ibrahim Harid.
Kamfanin dillancin labarai na Yaman ya sanar da bayanan da Shugaban Kasar Abdurrab Hadi Mansur ya fitar.
Mansur ya ce, an kashe Harid a harin ta'addanci da aka kai, kuma 'yan ta'addar da suka aikata hakan za su girbi abun da suka shuka.
Mataimakin gwamnan jihar Hudeyde Walid Al-Kudaymi ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya ce, an yi garkuwa da Harid a gaban gidansa da ke Aden.
Kafafan yada labarai sun ce an samu gawar Harid a Aden kuma an ga alamun ciwuka da aka ji masa kafin a kashe shi.