Sojojin Iran 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da suka yi da 'yan bindiga a arewa maso-yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA ya bayyana cewar a wajen garin Serdesht na jihar Azabaijan ta Yamma ne aka samu arangama tsakanin jami'an soji da 'yan bindiga inda aka kashe sojoji 3.
An bayyana kashe 'yan ta'adda da dama a rangamar da aka yi a kusa da kan iyakar Iran.
A labaran ba a bayyana su waye 'yan bindigar ba, amma a yankin an taba samun arangama tsakanin jami'an tsaron Iran da reshen 'yan ta'addar PKK na kasar PEJAK.