A lardin Dera da ke Kudancin Siriya an kashe sojojin gwamnatin Bashar al-Assad 21 wadanda tsoffin abokan hamayya suka kai musu harin kwanton bauna.
Wasu tsoffin abokan hamayya dauke da makamai sun kai harin kwanton bauna kan ayarin sojoji na runduna ta 4 karkashin jagorancin dan uwan Bashar Assad, Mahir Assad a kusa da garin Miziyrip da ke yammacin yankin Dera.
Yayin da aka kashe sojojin gwamnati 21 a take, wasu da dama sun samu raunuka a rikicin.
Don haka, gwamnatin Assad ta yi asarar rayuka mafi girma a yankin tun Yulin shekarar 2018, lokacin da ta mamaye lardin Dera.