An sanar da kashe shugaban kungiyar Azavad ta CMA Sidi Ibrahim Ould Sidati wacce tarayyar Tuareg masu rinjaye ta kafa a kasar Mali.
Kamar yadda kafafen yada labaran cikin gida, wasu 'yan bindiga ne suka kaiwa Ould hari a gidansa dake Bamako inda suka yi masa munanan raunukan da aka garzaya da shi asibiti inda ya rasu.
A lokacin da aka bayyana afkuwar lamarin ba'a yi nasarar kame ko dora alhakin harin akan kowa ba.
A kasar da aka kwashe shekaru ana fama da rikice-rikice, al'umman Tuareg sun kafa kungiya a shekarar 2014 da ta yi sulhu tsakanin gwamnati da 'yan bindiga a ranar 15 ga watan Mayun 2015.