An kashe sakataren wata gunduma a Afganistan

An kashe sakataren wata gunduma a Afganistan

Sakataren gundumar Washir da ke jihar Helmand din Afganistan Muhammad Zahir Haykar ya rasa ransa sakamakon kisan da aka yi masa ta hanyar harbi da bindiga.

Gwamnan jihar Abdul Nabi Elham ya shaidawa manema labarai cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kan Haykar a garin Lashkergah na Helmand.

Elham ya ce, Haykar ya rasa ransa sakamakon harin, kuma an fara kokarin kamo maharan.

Shaidun gani da ido sun ce, Sakataren da karin wasu mutane biyu ne suka mutu sakamakon harin.

Babu wanda ya dauki alakin kai harin.


News Source:   ()