Mutum 1 ya rasa ransa, wani 1 ya jikkata sakamakon hari da bindiga da aka kai a kofar wani asibiti da ke Paris Babban Birnin Faransa.
Maharin ya tsere a kan babur.
'Yan sanda sun bayyana cewa, an kai wanda aka jikkata zuwa asibitin Henru Dunant.
Tashar talabijin ta BFM ta sanar da cewa, wanda aka kashe din namiji ne, wanda aka jikkata kuma wata mace ce da ke aikin gadi a asibiti.
Har yanzu ba a san musabbabin kai harin ba.