Mutane 8 sun mutu sakamakon kisan kai da aka yi musu yayin bikin Kirsimeti a Bogota, babban birnin Colombia.
Jaridar El Tiempo ta ruwaito cewa an kashe mutane 8 a sassa daban-daban na birnin yayin bikin Kirsimeti a Bogota.
Jami’ai tsaro sun bayyana cewa yawan kashe-kashen ya ragu da kashi 76 cikin 100 idan aka kwatanta da Kirsimeti a bara.
Bugu da kari, daga cikin wadanda suka karya dokar hana fita waje da aka saka a birnin Bogota domin dakile yaduwar cutar har su 1,202 an yanke musu tara.