Mutane 10 sun rasa rayukansu, wasu 12 sun jikkata sakamakon harin da aka kai a Kabul Babban Birnin Afganistan.
Kakakin M'aikatar Harkokin Cikin Gida Hamid Rushan ya shaida cewa, an kai hare-haren a yankunan Sari Kariz da Golai Dawahane da ke Kabul.
Rushan ya bayyana an kashe fararen hula 10 tare da jikkata wasu 12 sakamakon hare-haren na bam da aka kai a lokaci guda.
Rushan ya kara da cewa, an nufi fararen hula a hare-haren wanda wannan laifin yaki ne.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin