An kashe mutane 9 a harin bam a Afrin

Mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai da mota a shingen binciken ababan hawa na gundumar Afrin da ke hannun 'yan adawa a arewacin Siriya.

An tayar da bam din da aka saka a cikin wata motar akori-kura a yankin da dakarun Turkiyya suka tsaftace daga 'yan ta'adda a karkashin Farmakan Reshen Zaitun da aka kaddamar a shekarar 2018.

Rahotannin farko da aka samu sun ce mutane 9 ne suka mutu yayinda wasu 43 suka jikkata sakamakon harin.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewar 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK ne suke kai hare-haren bam a yankin, amma saboda suna kashe fararen hula ya sanya ba sa daukar alhakin kai hare-haren.

'Yan ta'addar YPG/PKK da aka amince za su bar yankin Tel Rifat karkashin yarjejeniyar da Turkiyya da Rasha suka kulla a watan Oktoban 2019, suna yawan kai hare-haren bam a gundumomin Bab, Azez, Jarabulus da Afrin.


News Source:   ()