Mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren bindiga da aka kai a wasu dakunan tausa da ke jihar Georgia ta Amurka.
Labaran da jaridun Amurka suka fitar na cewa, bayanan da suka samu daga 'yan sandan Atlanta sun bayyana kaiwa Asiyawa hari a yankin Cherokee da ke arewacin Atlanta inda aka kashe mutane 4.
Jim kadan bayan kai harin ne aka sake samun labarin yunkurin yin sata a tsakiyar garin Atlanta, inda barawon ya bude wuta a dakin yin tausa tare da kashe mutane 3. Jim kadan da faruwar hakan aka sake kai hari a wani dakin yin tausar inda a nan ma aka kashe mutum 1.
'Yan sandan da suka gudanar da bincike sun bayyana kama maharin mai suna Robert Aaron Long, kuma an gano Long ne ya kai dukkan hare-haren 3.
Ana ci gaba da bincike kan harin, kuma kafafan yada labarai na Amurka sun bayyana cewa, 6 daga cikin wadanda suka mutu mata ne 'yan asalin Asiya.