Jami'an tsaro 7 da farar hula 1 sun rasa rayukansu sakamakon harin bindigu da na bam da 'yan tawayen Taliban suka kai a jihar Belh da ke arewacin Afganistan.
Kakakin 'yan sandan jihar Belh Adilshah Adil ya fadi cewar 'yan tawayen sun binne bam a gefe hanya a ungumar Alem Hil da ke gundumar Belh ta jihar Belh, bam din ya fashe a lokacin da motar jami'an tsaro ta ke wucewa, kuma bayan fashewar 'yan tawayen sun bude wuta da bindigu a yankin.
Adil ya ce jami'an tsaro 7 da farar hula 1 ne suka mutu, wasu fararen hula 6 kuma suka jikkata sakamakon hare-haren, a arangamar da ta biyo baya 'yan tawayen ma sun tafka asara.
Kungiyar Taliban ba ta ce komai ba game da lamarin.