An kashe mutane 7 sakamakon hari da bindiga da aka kai a wajen bukin ranar haihuwa a garin Colorado Springs dake Amurka.
Labaran da jaridun Amurka suka fitar sun bayyana cewa, a lokacin da 'yan sanda suka je wajen sun tarar da mutane sun mutu, inda mutum 1 da ya jikkata ua mutu bayan an kai shi asibiti.
An bayyana cewa, wanda ya kai harin saurayin daya daga cikin wadanda suka mutu ne.