Mutane 6 da suka hada da yaro karami 1 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai da bindiga a Amurka.
An kashe mutane 4 da suka hada da yaro 1 a harin da aka kai da bindiga a wata cibiyar saye da sayarwa da ke garin Orange na jihar California.
An kama maharin bayan jikkata shi da aka yi a musayar wutar da suka yi da 'yan sandan da aka tura wajen.
A hari da bindiga da aka kai a kusa da tashar jiragen kasa ta Washington kuma an kashe mutane 2 tare da jikkata wasu 3.
'Yan sanda sun fara gudanar da bincike, kuma ba a bayyana waye ya kai harin ba.