Mutane 5 daga iyali 1 sun rasa rayukansu sakamakon hari da bindiga da aka kai a Mekziko.
Wasu mutane da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kan wani gida a garin Irapuato na gundumar Guajunato inda suka kashe mata 4 da namji 1.
Mahukunta sun ce, maharan sun je gidan da motoci inda suka bude wuta kan iyalan tare da guduwa.
An fara gudanar da bincike don kamo maharan.