Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon hari da bindiga da aka kai musu a Kolombiya.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce, a kauyen La Piedra na garin Andes da ke yankin Antioquia ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kai hari da bindigu kan wani gidan gona tare da kashe mutane 5, wasu da dama kuma sun jikkata.
An fara gudanar da bincike game da lamarin.