An kashe mutane 5 a Afganistan

An kashe mutane 5 a Afganistan

Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai a wani gida da ke gundumar Isma'il Hil din jihar Host da ke Afganistan.

Kakakin 'yan sanda Host Adil Haydari ya ce maharan da ba a an ko su waye ba sun kai hari kan wani gida a kauyen Digan na gundumar Isma'ila Hil.

Haydari ya ce maharan sun kashe mutane 5 tare da jikkata wasu 3 a gidan.

Ya kara da cewar maharan sun gudu daga yankin, kuma an fara gudanar da bincike.

Babu wani ko wata kungiya da suka dauki alhakin kai harin.


News Source:   www.trt.net.tr