An kashe mutane 4 sakamakon harin bindiga a Amurka

An kashe mutane 4 sakamakon harin bindiga a Amurka

Mutane 4 da suka hada da jariri 1 sun rasa rayukansu sakamakon harin bindiga da da wani tsohon ma'aikacin rundunar sojin ruwa ya kai a jihar Florida ta Amurka.

An bayyana cewa, maharin ya kuma jikkata wata yarinya mai shekaru 11 a rikicin da ya barke a yankin Tampa na Florida.

Jaridun Amurka sun bayyana cewa, maharin ya mika kansa ga jami'an tsaro kuma cutar damuwa da kunar zuci na damun sa.

 


News Source:   ()