An kashe mutane 4 sakamakon harin bam a Afganistan

An kashe mutane 4 sakamakon harin bam a Afganistan

Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a jihar Kandahar da ke kudancin Afganistan.

Shugaban 'Yan sandan Kandahar Jamal Nasir Barikzey ya shaidawa manema labarai cewar wani bam da aka binne a gefen hanya ne ya fashe a lokacin da mota dauke da fararen hula ta ke wucewa a kauyen Zela Han na gundumar Pancvayi da ke jihar ta Kandahar.

Barikzey ya ce fararen hula 4 sun mutu sakamakon harin, wasu 6 kuma sun samu saunuka.

Babu wani kowata kungiya da suka dauki alhakin dasa bam din.


News Source:   ()