An kashe mutane 4 sakamakon harin 'yan bindiga a Amurka

An kashe mutane 4 sakamakon harin 'yan bindiga a Amurka

Mutane 4 sun rasa rayukansu, wasu 13 sun samu raunuka sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai a garin Cincinnati na jihar Ohio da ke Amurka.

Mataimakin Daraktan 'Yan sandan yankin Paul Neudigate ya shaida cewar an kai hari a wurare uku daban-daban da ke garin.

Neudigate ya ce 4 daga cikin mutane 17 da aka jikkata sakamakon hare-haren sun rasa rayukansu.

An bayyana cewar hare-haren ba su da alaka da juna.


News Source:   ()