Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a Kabul Babban Birnin Afganistan.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Tarik Aryan ya shaidawa manema labarai cewa, wani bam da aka saka a cikin motar Kakakin Sashen Tsaron Jama'a Ziya Vadan ya fashe a yankin Karte Nev da ke Kabul.
Aryen ya shaida cewar, Vadan da wasu abokansa biyu sun mutu yayinda wani mutum 1 kuma ya samu rauni.
Kakakin ya dora alhakin harin kan 'yan Taliban.
Babu wani da ya fito ya dauki alhakin kai harin.