Jami'an tsaro 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da 'yan tawayen Taliban suka kai a gundumar Geh Yak din jihar Gazne da ke Afganistan.
Kakakin Fadar Gwamnan Gazne Wahidullah Jumazada, ya shaida cewar 'yan tawayen sun kai hari da mota dauke da bam a tsakiyar gundumar Deh Yak.
Jumazada ya fadi cewar jami'an tsaro 3 sun rasa rayukansu, wasu mutanen 9 sun samu raunuka sakamakon harin. Kuma Taliban ma ta yi asarar mambobinta a arangamar da ta biyo bayan tashin bam din.
Babu wata sanarwa da Taliban ta fitar game da batun.