Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon hari da bindiga da aka kai a wani babban kanti da ke jihar Florida ta Amurka.
Ofishin 'yan sandan yankin Palm Beach ya fitar da sanarwa ta shafin Twitter cewa, an kai hari da bindiga a kantin Publix da ke garin Royal Palm Beach.
An bayyana cewa, a lokacin da 'yan sanda suka je wajen sun tarar da gawarwakin mutane 3 da suka hada yaro karami 1 da mata 2.
Ba a bayar da bayanai kan musabbabin kai harin da kuma waye maharin ba, amma an fadi cewa jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike.