Mutane 2 ne suka rasa rayukansu sakamakon hari da bindiga da aka kai a garin Espelkamp na jihar North-Ren Vestfalya da ke Jamus.
Kamfanin dillancin labarai na Jamus (DPA) ya samu bayanai daga 'yan sandan yankin da ke cewa, an kai hari da bindiga a tsakiyar garin Espelkamp.
Mutane 2 sun mutu sakamakon harin, maharan kuma sun gudu.
An dauki tsauraran matakan tsaro a yankin.