An kashe mutane 2 a hari da wuka a Faransa

An kashe mutane 2 a hari da wuka a Faransa

Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon hari da wuka da aka kai a kusa da wata Majami'a da ke garin Nice na Faransa.

Shugaban gundumar Nice Christian Estrosi ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa, an kama wanda ya kai harin da wuka a kusa Majami'an Notre Dame.

Estrosi ya bayyana harin a matsayin na ta'addanci.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa gerald Darmanin ya ce 'yan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin.


News Source:   ()