An kashe mutane 2 a Afganistan

An kashe mutane 2 a Afganistan

Ma'aikatan gwamnati 2 sun rasa rayukansu sakamakon hari da bindiga da aka kai musu a jihar Gazne da ke Afganistan.

Kakakin helkwatar 'yan sandan Gazne Ahmad Han Siret ya shaida cewa, wasu ma'aikatan ofishin aje bayanai na gwamnatin jihar Gazne ne aka harbe da bindiga har lahira.

Siret ya ce, mutanen 2 sun mutu kuma maharan sun gudu daga yankin.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

 


News Source:   ()