A watanni 6 na farkon shekarar 2020 an aikata kisan gilla ga mata 489 a kasar Mekziko.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce rahoton da ofishin magatakardar gwamnati ya fitar ya bayyana mutuwar mata 489 ta hanyar kisan gilla a tsakanin watan Janairu da Yunin 2020.
Masu fafutuka da dama sun taru a gaban Fadar gwamnatin Kasa da ke Babban Birnin Mexico City don nuna adawa da daduwar kashe mata da ake samu a kasar a 'yan watannin nan.
Kungiyoyin farar hular masu fafutuka tare da dalibai sun dinga daga allunan da akada aka rubuta "Idan ba samar da mafita ba, ba za mu daina zanga-zanga ba" da "Abin takaici adalci karami".
Mekziko ce kasar Latin Amurka da aka fi samun laifukan kisan kai ga mata.