Ma'aikatan shari'a 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon hari da bindigu da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai a gundumar Deh Zebz da ke Kabul Babban Birnin Afganistan.
Kakakin helkwatar 'yan sandan Kabul Firdaws Faramarz ya shaida cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kan Ofishin Gabatar da Kara na Afganistan.
Ya ce an kashe lauyoyi 2 da wasu ma'aikatan gwamnati 5 a harin da aka kai da bindigu, kuma maharan sun gudu daga yankin.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.