An kashe jami'an tsaro 7 a Afganistan

Sojoji 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai wa sansaninsu da wata mota makare da bama-bamai.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Afganistan Tarik Aryen ya shaida cewar an kai hari da mota dauke da bama-bamai kan sansanin soji da ke yankin Kotal Ravza.

Aryen ya ce an kashe jami'an tsaro 7 tare da jikkata wasu 16 a harin.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.


News Source:   ()