Jami'an tsaro 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan tawayen Taliban suka kai kan ofishin 'yan sanda na jihar Bamyan din Afganistan.
Gwamnan Bamyan Sa'id Anwar Rahmeti ya shaida cewa, 'yan tawayen sun kai hari kan cibiyar 'yan sanda a gundumar Kuhmerd dake jihar.
Rahmeti ya kara da cewa, an kashe jami'an tsaro 5 tare da jikkata wani 1 sakamakon harin.
Gwamnati Rahmeti ya kuma ce, an samu arangama tsakanin bangarorin 2 a yayin kai harin inda aka kayiwa Taliban barna.
Sanarwar da Taliban ta fitar ta ce, sun kashe 'yan sanda 9 a harin.