An kashe jami'an leken asirin Afganistan 7

An kashe jami'an leken asirin Afganistan 7

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai da bam kan ginin hukumar Leken Asiri ta Afganistan da ke jihar Gazne.

Kakakin fadar gwamnan Gazne Wahidullah Jumazadeh ya fada wa manema labarai cewar maharin ya kai hari kan ginin Hukumar Leken Asiri da wata mota da aka dasa bama-bamai a cikinta.

Jumazadeh ya ce an kashe jami'an leken asiri 7 tare da jikkata wasu 40 a harin.

Kakakin ya kara da cewar 8 daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali, kuma ana fargabar adadin wadanda za su mutu zai karu.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.


News Source:   www.trt.net.tr