Fararen hula 6 da suka hada da yara kanana 3 ne suka rasa rayukansu yayinda wasu 7 suka jikkata sakamakon harin ta'addanci da aka kai da mota dauke da bama-bamai a yankin Tel Abyad da ke hannun'yan adawa a arewacin Siriya.
An samu fashewar abubuwa a tsakiyar gundumar Tel Abyad da dakarun Turkiyya da Dakarun Kasa na Siriya suka tsaftace daga 'yan ta'adda a lokacin kai Farmakan Tafkin Zaman Lafiya.
Sakamakon fashewar bama-baman da aka saka a cikin wata mota, bayanan farko sun ce fararen hula 6 da suka hada da yara kanana 3 sun mutu, wasu mutanen 7 kuma sun samu raunuka.
An kai 4 daga cikin wadanda suka jikkata da ke cikin mawuyacin hali zuwa asibitin Turkiyya.
Wuraren sana'a da ke kewayen wajen da aka kai harin sun samu matsala.
Jami'an staro da suka gudanar da bincike a wajen sun ce ana kyautata zaton 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK ne suka kai harin.