Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani bam da aka binne a gefen hanya a jihar Helmand da ke Afganistan.
Kakakin Fadar Gwamnan Helmand Umar Zuwak ya shaida cewa, a garin Leshkergah ne aka dasa bam a gefen hanya wanda ya fashe a lokacin da mota dauke da fararen hula su ke wucewa.
Zuwak ya shaida cewa, an kashe farare hula 5 sakamakon fashewar bam din.
Mahukunta sun dora alhakin lamarin kan 'yan tawayen Taliban.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.