Fararen hula 5 da suka hada da yara kanana 2 sun rasa rayukansu sakamakon harba makamin roka da 'yan tawayen Taliban suka yi a jihar Gazne da ke Afganistan.
Rahotanni sun ce makamin ya fada kan wani gida tare da kashe fararen hula 5.
Kakakin fadar gwamnan Gazne, Wahidullah Jumazadeh ya fadi cewar 'yan tawayen Taliban sun yi arangama da jami'an tsaro a kauyen Sere na gundumar Ender.
Ya ce sakamakon harba maamin roka da Taliban ta yi a yayin arangamar wanda ya kuma fada kan wani gida, fararen hula 5 da suka hada da yara kanana 2 sun mutu.
Babu wata sanarwa da Taliban ta fitar game da wannan ikirari.
A wani hari da makamin roka da aka kai a Kabul Babban Birnin Afganista an jikkata mutane 10.