Fararen hula 28 ne suka rasa rayukansu, wasu 13 kuma suka jikkata sakamakon harin da aka kai wa wata motar bas a Siriya.
Kamfanin dillancin labarai na Siriya (SANA) ya bayyana cewar, da misalin karfe 16.00 na ranar Larabar nan ne aka kai hari kan motar bas dauke da fararen hula a kan hanyar Deyruzzor-Tedmur da ke yankin Kebajib.
A labaran an bayyana kashe fararen hula 28 tare da jikkata wasu 13.
An sanar da cewar, maharan sun fito daga yankin Tanf da ke hannun dakarun Amurka a iyakar Siriya da Jordan, kuma sun bace a sahara bayan kona motar da fararen hula ke ciki.