An kashe fararen hula 125 a watan da ya gabata a Siriya

An kashe fararen hula 125 a watan da ya gabata a Siriya

Rundunar Kare Hakkokin Dan Adam ta Siriya ta bayyana cewar a watan da ya gabata a kasar an kashe fararen hula 125 da suka hada da yara kanana 26 da mata 6.

Sojojin gwamnatin Asad sun kashe fararen hula 10 da suka hada da mata 2, Rasha da ke taimakawa gwamnatin kuma ta kashe farar hula 1.

Kungiyar ta'adda ta YPG/PKK ta kashe farare hula 7 da suka hada da yara kanana 2 a watan da ya gabata a Siriya.

'Yan adawa masu dauke da makamai sun kashe 3, sojoji masu adawa kuma sun kashe wasu fararen hular 7.

Rahoton ya kuma ta batun mutanen da aka kashe ta hanyar azabtar da su, inda gwamnatin Asad ta kashe 7, kungiyar ta'adda ta YPG/PKK kuma ta kashe wani mutum 1.

Rahoton ya ja hankali da cewar wasu fararen hula 97 da suka hada da mata 22 da yara kanana 3, sun rasa rayukansu sakamakon bama-baman da suka fashe wadanda ba a san wanne bangare ne ya dasa su ba.


News Source:   www.trt.net.tr