A kasar Ethiopia jami'an wani yanki sun yi ikirarin cewa 'yan tawayen Tigray People Liberation Front (TPLF) sun kashe fararen hula fiye da 120 a lardin Amhara.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya sanar, Sewunet Wubalem, daraktan yankin Dabat, inda aka yi kisan gillar, ya bayyana cewa sun gano gawawwaki 123 da kungiyar ta TPLF ta kashe zuwa yanzu kuma suna fargabar cewa wannan adadin zai karu.
Wubalem ya lura cewa an kai harin ne bayan yunkurin da kungiyar ta TPLF ta yi na kwace birnin Gondar a ranar 27 ga watan Agusta.
"Yara, iyaye mata, har ma da shugabannin addini an kai musu hari."
Kungiyar ta TPLF, wacce ta kai hare -haren a lardunan Amhara da Afar a cikin ‘yan watannin nan domin gwamnati ta janye shingen da ta sanyaa Tigray, a baya an zarge ta da aikata kisan kiyashi a yankuna daban -daban.
A gefe guda kuma, kungiyar TPLF ta yi ikirarin cewa mutane 150 ne suka mutu sakamakon yunwa a jihar Tigray sakamakon shingen da aka sanya da ya hana shige da fita a yankin.