An bindige wani dan bindiga dadi a yayinda yake bude wuta a sansanin sojin saman Amurka na Corpus Christi dake birnin Texas.
Dangane ga bayanan da suka fito daga rundunar sojin ruwan Amurkja, maharin ya kai hari da misalin karfe 06.15 a sansanin sojin saman Corpus Christi.
Sanarwar ta kara da cewa a yayinda aka magance maharin soja daya kuma ya raunana.
Jami'in hukumar bincike ta (FBI) Leah Greeves ya sanar da cewa an kame maharin a mace kuma abokan ta'asarsa sun tsere.
Jami'i Greeves ya bayyana cewa harin ta'addanci ne sai dai yaki bayyna dalilin da ya sanya suke ganin hakan.