An sanar da kashe babban kwamandan 'yan ta'addar Daesh a kasar Iraki.
Sanarwar da aka fitar daga sashen yaki da ta'addanci na Iraki ta ce a farmakan da aka kai an kashe shugaban 'yan ta'addar Daesh a kasar mai suna Mutaz Al-Juburi.
Sanarwar ta ce an kashe Juburi a yankin Deyrizzor na arewacin Siriya a yayin wasu farmakai ta sama da Kawancen Kasashen Duniya suka kai.
A ranar 30 ga watan Mayu ma gwamnatin Iraki ta sanar da kashe mutumin da aka aiyana a matsayin Khalifan Shugaban Daesh Al-Bagdadi da aka kashe, wato Abdulnasir Kardash.
A ranar 27 ga watan Oktoban 2019 ne Amurka ta kai farmaki a yankin Idlib na arewacin Siriya tare da kashe Al-Bagdadi.