A Afganistan an bayyana kashe babban jagoran 'yan ta'addar Daesh kuma mai kula da aiyukan leken asiri na kungiyar a yankin Horasan mai suna Asadullah Orukzey.
Rahotanni sun ce an kashe Orukzey a jihar Nangarhar da ke gabashin kasar ta Afganistan.
Sanarwar da Hukumar Kula da Tsaron Kasa ta Afganistan ta fitar ta ce Orukzey na daya daga cikin masu zubar da jini a kasar, kuma za su ci gaba da kai wa 'yan ta'addar farmakai don ganin bayan su.