A yankin da aka gudanar da Farmakin Tafkin Zaman Lafiya dake Siriya an yi nasarar kassara ‘yan ta’addar PKK/YPG 10.
Ma’aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta sanar da cewa, a daren 19 ga watan Mayu wasu gungun ‘yan ta’adda suka yi yunkurin yin kütse a yankin.
Sanarwar ta kara da cewa,
An yi nasarar gano ‘yan ta’addar PKK/YPG 10 ta hanyar aikin kwararrun kwamandojin sojin kasar Turkiyya.
Da haka an magance ‘yan ta’addar a yankin har guda 66 a cikin wata daya. Daga watan Janairu kawo yanzu kuwa an yi nasarar kassara ‘yan ta’adda 1445 a yankin baki daya.